Sakamakon wani bincike ya nuna cewa ‘yan siyasa na neman gurgunta Shirin Shugaba Muhammad Buhari na ba talakawa Naira dubu biyar a kowane wata inda suka yi katutu wajen zaben wadanda za su ci ajiyar shirin a jihohin da aka tsara aiwatar da shirin.
An dai tsara aiwatar da shirin ne a jihohin Borno, Kwara Bauchi, Cross River, Niger, Kogi, Oyo, Ogun da Ekiti sai binciken ya nuna cewa a jihar Kwara inda aka fara biyan kudaden, masu kula da shirin sukan bayar da 5000 ce ga iyalan gida guda sabanin yadda aka tsara ba mutum guda a cikin dangi.