Marburg ta hallaka mutum 2 a Ghana | Labarai | DW



A karon farko a kasar Ghana, an gano mutum biyu da suka mutu, bayan da suka kamu da cutar nan mai suna Marburg, cutar mai kaman-cece-niya da Ebola, nada alamomin da suka hada da mai da gudawa da kuma zazzabi. Tuni Hukumar Lafiya ta Duniya ta tura wata tawagar kwararru don ganin an taimaka ma kasar dakile cutar.

Kadan daga cikin abin da aka sani a game da kwayar cutar Marburg, tana da saurin yaduwa kuma kawo yanzu babu maganinta koma riga-kafinta. Ghana ta kasance kasa ta biyu a yankin yammacin Afirka da cutar ta bulla baya ga kasar Gini. Amma a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, an taba samun bullar cutar a kasashen Angola da Jamhuriyyar Demokradiyar Kwango da Kenya da Afirka ta Kudu da kuma Yuganda.
 



You may also like