
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Maroko ta sanar da hukumar kwallon kafa ta duniya cewa bata gamsu da bushin lafarin da ya jagoranci wasan da suka yi da Faransa ba ranar Laraba.
An cire Maroko a zagayen kusa da karshe na gasar cin kofin duniya ta Qatar 2022.
FMRF ta ce Lafari Cesar Ramos dan kasar Mexico ya hana su fenareti kafin aje hutun rabin lokaci, a lokacin da Theo Hernandez ya hada jiki da Sofiane Boufal a da’ira ta sha takwas.
A maimakon hakama sai ya bai wa Boufal katin gargadi cewa shi ne ya yi keta.
Kazalika Maroko ba ta ji dadin yadda aka yi gaggawar cire Selim Amallah ba, ba tare da an jira a yi bugun tazara ba kafin ya fita.
Maroko ta kafa tarihin zama kasar Afrika kuma ta Larabawa ta farko da ta taba zuwa zagayen kusa da karshe a gasar cin kofin duniya.
Sanarwar da FMRF ta fitar ta ce ”FMRF na bukatar a yi duba kan bushin da ya hana wa Maroko bugun fenareti har sau biyu.”
Ta kara da cewa ”Hakama FMRF ta kadu da yadda alkalan da ke lura da na’urar VAR suka nuna cewa ba suga abinda ya faru ba.”
Masu sharhi da dama kamar Chris Sutton ya ce ya yi mamakin yadda na’urar VAR ta hana Maroko bugun fenareti.
A cewar Sutton wanda ke aiki da BBC a Qatar ya ce ” na zaci fenareti aka bai wa Boufal na keta da aka yi masa.
Har yanzu Maroko na da wasa daya da ya rage musu da Croatia ranar Asabar, inda anan za a tantace wanda zai zo na uku a gasar.
Sai kuma ranar Lahadi inda za a buga wasan karshe tsakanin Argentina da Faransa, wadda ta doke Maroko 2-0.
Maroko ta bada mamaki bayan da ta doke Belgium da Sfaniya da Portugal kafin ta kafa tarihin zuwa zagayen kusa da karshe.