
Asalin hoton, OTHER
Tsohon kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya Gernot Rohr, ya ce a halin da ake ciki Maroko ta dade da yi wa Najeriya nisa a fagen ci gaban kwallon kafa.
Rohr ya fada wa jaridar Augsburger-Allgemeine cewa, ”rashin kayan wasanni da suka hada da filayen atisaye da karanci koyar da ilimin ita kanta kwallon kafa a Najeriya babban cikas ne gareta dama wasu kasashen Afrika.”
” Mafi yawancin kungiyoyin kwallon kafa a Najeriya basu da matakin kananan yara duk da kasar na da matasa da suka iya kwallo.”
”Makarantun kwallo na yan kasuwa ne kawai ke kokari, kuma suma neman kudi ne ya dame su, na suga cewa sun samar da kwararru,” in ji Rohr.
A watan Disamban 2021 ne Super Eagles ta raba gari da Gernot Rohr, kuma ya ce bai yi mamakin abunda Maroko ta yi ba a gasar kofin duniya ta Qatar 2022.
Maroko ta kafa tarihin zama kasar Afrika ta farko da ta kai zagayen kusa da karshe a gasar kofin duniya, bayan da ta doke kasashen Turai masu karfi kamar Belgium, da Sfaniya da kuma Portugal.
To amma masana na ganin ba abun mamaki bane irin nasarar da Maroko tayi, idan aka yi la’akari da jarin da ta zuba wurin inganta harkar kwallon kafa tsawon shekaru.