Martanin Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Kan Da’awar Saudiya


 

Kakakin kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya ce da’awar da Saudi-Arabiya ta yi na cewa kungiyar ta kai hari kan garin Makka, yunkuri ne na sanya rudani a tsakanin Al’ummar musulmi.

Tashar Telbijin din Almasira ta kasar Yemen ta nakalto kakakin kungiyar Ansarullah Muhamad Abdussalam a jiya Juma’a na cewa muna bukatar Al’ummar musulmin Duniya da su yi watsi da karyace-karyacen  kawancen masarautar Ali-sa’oud, su yi aiki da abinda yake na gaskiya,

Abdussalam ya kara da cewa musulinicin Al’ummar kasar yemen abu ne da ba ya bukatar a tabbatar da shi  Duniya, kuma duk da irin hasarar rayuka da Dukiya da kasar ta fuskanta har yanzu babu wata cibiya ta fararen hula a kasar Saudiyan da suka kaiwa hari, ba rantana wuraren masu tsarki.

Domin sanya rudani a tsakanin Al’ummar musulmi, a safiyar jiya Juma’a  magabatan Saudiya suka sanar da cewa an halbo wani makami mai lizami daga birnin Sa’ada na kasar Yemen zuwa garin Makka, lamarin da jami’an tsaron  kasar Yemen din suka karyata.

Saidai a matsayin mayar da martani kan irin ta’addancin da kawancen saudiya ke yi a kasar ta Yemen, Dakarun tsaron kasar sun halba makamai masu lizzami a wuraren jami’an tsaron kasar dake birinin Jedda, inda wasu rahotanni ke cewa wani makami mai lizzami ya fada filin sauka da tashi na jiragen saman Malik Abdul-Aziz dake birnin Jeedda ranar Alkhamis din da ta gabata.

You may also like