
Asalin hoton, Getty Images
Gabriel Martinelli
Ɗan wasan gaba na Brazil Gabriel Martinelli, 21, ya ƙulla sabuwar yarjejeniya da Arsenal wadda za ta ba shi damar ci gaba da zama a ƙungiyar har 2027. (Athletic – subscription required)
Bayanai na cewa Newcastle United ta shiga sahun masu rige-rigen sayen mai buga wa Ingila tsakiya Jude Bellingham,19, daga Borussia Dortmund. (Football Transfers)
Todd Boehly, ya fusata Fiorentina bayan da mai Chelsea ɗin ya ƙudiri aniyar ƙoƙarin sayen ɗan wasan Morocco na tsakiya Sofyan Amrabat, 26, a matsayin aro a ranar da aka rufe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo. (New York Times via Talksport)
River Plate ta shirya karɓar kusan £28m sakamakon komawar ɗan wasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez mai shekara 22 zuwa Chelsea daga Benfica. (Fabrizio Romano via Twitter)
A wani labarin kuma, ƴan wasan Chelsea na gida na fargabar ƙungiyar za ta cefanar da su domin kaucewa shiga tarkon hukumar kula da kudaden da kulob-kulob ke kashewa, FFP idan Blues ta gaza samun tikitin gasar Zakarun Turai a wannan kakar. (Telegraph – subscription required)
Tottenham ta kusa kammala tattaunawar sayen dan wasan gaba na Spaniya Gerard Deulofeu, 28, kafin cire shi daga ci gaba da taka leda saboda raunin da ya ji a gwiwa. (Fabrizio Romano via Express)
Wakilin Moises Caicedo, 21, ya soki Brighton saboda ƙin amincewa ɗan wasan tsakiyar na Ecuador ya koma Arsenal inda ya ce ba za su sake maimaita irin haka ba a rayuwa. (Marca90 via Ole – in Spanish)
Ana sa ran cikin ƴan kwanaki masu zuwa, ɗan wasan Ingila Jack Harrison, 26, zai sabunta kwantiraginsa a Leeds United in the coming weeks. (Sky Sports)
Har yanzu mai buga wa Spaniya tsakiya Isco, 30, yana neman sabon kulob, an kuma yi tayinsa a wasu ƙungiyoyin Premier da dama kan yarjejeniya ta gajeren lokaci. (90min)
Yayin da Everton ke duba yiwuwar sayen Isco, ƙungiyar ta bayyana damuwa kan ko tsohon ɗan wasan Real Madrid yana da ƙwarin da ake buƙata don taka leda a gasar Ingila. (Independent)
Juventus na duba yiwuwar cefanar da ko ma kawo ƙarshen kwantiragin ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 29, Paul Pogba. (Mail)
Ana sa ran ɗan wasan Faransa Olivier Giroud, 36, zai tsawaita kwantiraginsa a AC Milan da shekara ɗaya har zuwa 2024. (Sport.Sky – in Italian)