Martinelli ya saka hannu kan zai ci gaba da taka leda a ArsenalMartinelli

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Arsenal, Gabriel Martinelli ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Emirates.

Dan kwallon Brazil, mai shekara 21 ya koma Emirates daga Ituana ta Brazil a kakar 2019, wanda kawo yanzu ya buga karawa 111 a dukkan fafatawa.

Dan wasan na taka rawar gani a Arsenal a kakar nan, wanda ya ci kwallo bakwai da suka taimaka kungiyar ke matakin farko a Premier League.

Arsenal tana ta daya a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester City ta biyu mai rike da kofin.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like