Matar nan da ta kashe mijinta kwanaki, Maryam Sanda ta roki kotu ta bayar da belinta saboda tana dauke da juna biyu na mijin nata, Marigayin Bilyaminu Mohammed Bello.
Tun a watan Nuwamba ake tsare da Maryam Sanda a gidan kurkukun Suleja bayan da kotu ta ki bayar da belinta sakamakon kashe mijinta wanda dan tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Dakta Bello Haliru ne.