
Asalin hoton, Getty Images
Sashen Labaran Yanayi da Kimiyya na BBC
Wani kwaɗo da ke rikiɗa ya koma akasari kamar jikin tangaran idan yana barci, mai yiwuwa zai iya ba mu haske kan fahimtar kamewar jini a jikin ɗan adam.
Tun can da daɗewa masana kimiyya suna da masaniya game da kwaɗo mai jikin tangaran amma ba su iya fahimtar yadda yake rikiɗa har ake iya ganin cikin cikinsa ba.
Yanzu bincike ya gano cewa kwaɗon yana iya kwaranyewa ko tsinka jini a jikinsa, ba tare da hakan ya zame masa illa ta hanyar kamewa a wuri ɗaya ba.
Sakamakon zai iya bunƙasa fahimtar aikin likitanci game da kamewar jini mai hatsari – wata babbar larura da ta zama ruwan dare.
Kwaɗon mai jikin tangaran – wanda bai fi girman dunƙulen alewa ba – yakan shafe tsawon kwanaki yana barci a jikin korayen ganyaye masu walƙiya a yankin Turofik.
To, don ya kaucewa idon dabbobi ‘yan farauta, sai ya rikiɗe ya mayar da fiye da kashi 61 na gangar jikinsa tamkar kwalba, inda zai saje da jikin ganye.
Asalin hoton, JESSE DELIA
Kwaɗi masu jikin tangaran suna barci ne kan ganyaye bayan jikinsu ya koma gani har hanji amma dabbobi masu farauta ba sa iya ganin su
“Idan da za ku juya kwaɗon, ku kifa shi rigingine, kuna iya ganin zuciyarsu tana bugawa da kanta.
Za ku iya ganin har abin da ke ƙarƙashin fatar jikinsa, ku ga tsokar jikin, da mafi yawan lungu da saƙo na jikin duk ana iya ganin su garai-garai,” Jesse Delia, wani mai bincike a Gidan Adana Tarihi na Museum of Natural History a New York, ya faɗa wa BBC.
Yanzu binciken Mista Jesse Delia da Carlos Taboada na Jami’ar Duke a Amurka ya gano yadda kwaɗo mai jikin tangaran yake aiwatar da wannan abin ba sabon ba.
Ta hanyar haska mabambantan haske a kan nisan da ke tsakanin tudu da tudu na gangar jikin dabbobin a lokacin da suka farka da kuma a lokacin da suke barci, masanan kimiyyar sun auna yawan sashen cikin jikin da ido yake iya gani.
Da haka sun gano cewa waɗannan halittu suna kwaranye jininsu zuwa cikin hanta.
“Suna iya kwaranye mafi yawan jajayen ƙwayoyin halittun jini zuwa cikin hanta, su ware su daga cikin farin ruwan jini. Kuma za su ci gaba da amfani da farin ruwan jini wanda ke kai komo a sassan jiki… amma suna iya yin haka ne ba tare da sun janyo gagarumar kamewar jinin ba,” Mista Jesse Delia ya bayyana.
Asalin hoton, JESSE DELIA
Kwaɗon na shiga mabambantan matakai na kai komon jajayen ƙwayoyin halittun jini a lokacin da yake barci da kuma idan ya farka
Sama da kashi 89% na ƙwayoyin halittun jinin kwaɗon na dunƙulewa wuri guda, inda girman hantarsa zai ƙaru, ta kumbura har ta kusan ninka girmanta, abin da zai ba da dama a riƙa ganin har cikin cikin kwaɗon.
Da dare, idan dabbar tana so ta sake farkawa don zuwa kiwo ko barbara, sai ta saki jajayen ƙwayoyin halittun jini, su tafi su ci gaba da kai komo a jiki, ita kuma hanta sai ta sake laƙumewa.
Mista Taboada ya yi bayanin cewa jinin kwaɗon yana iya kamewa a duk lokacin da ya zama dole, ga misali idan ya ji rauni.
Wannan hikima ta zaɓin lokacin tsinka jini da kuma sanya shi ya kame, “wata zaƙaƙurar baiwa ce” da wannan halitta ke ita, in ji shi, kuma hakan zai iya buɗe kafa don inganta fahimtar kamewar jini ga ɗaukaci.
Ga mafi yawan dabbobi, kwaranye jini gaba ɗaya na iya haddasa kamewarsa, abin da kuma zai iya zama barazana ga rayuwa, ga misali hakan zai iya janyo bugawar zuciya ga ɗan adam.
Sai dai masu binciken sun jaddada cewa mayar da wannan ilmi zuwa amfani da shi a zahiri cikin harkar likitancin ɗan adam na iya shafe tsawon gomman shekaru.
An dai wallafa wannan bincike a mujallar harkokin kimiyya ta Science.