Masana kimiyyar sadarwa sun bukaci masu amfani da shafukan sadarwa da suyi hattara. 


Wani bincike da masana a fannin sadarwar zamani suka gudanar, ya gano cewa yanayin yadda ake amfani da kafofin sada zumunta a Najeriya na da hadari.
Abdulganiu Rufa’I Yakubu, jami’i ne a cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’uma a Najeriya, ya kuma ce abubuwan da suka gano a binciken da suka yi ka iya haifar da tashin hankali.

“Kafin mu fara bincikenmu sai da muka kira masana daga kasashe irinsu Kenya da Rwanda, wadanda irin wadannan kalaman ne suka sa aka yi asarar rayuka.” In ji Yakubu.

A baya wasu ‘yan majalisun Najeriya sun nemi a samar da wata doka, wacce za ta sa ido kan masu amfani da kafafan sada zumunta na zamani domin cin zarafin mutane ko kuma furta kalaman da za su harzuka jama’a.

Kasashe da dama da suka ci gaba, kamar China, suna da irin wadannan dokoki domin hana masu amfani da kafar sada zumunta da ke muzgunawa mutane.

A farkon shekarar nan rundunar ‘yan sandan Ghana ta ce ta na duba yuwuwar takaita amfani da kafofin sada zumunta domin tabbatar da tsaro yayin da kasar ke shirin gudanar da zabe a karshen shekarar nan.

Saurari rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad daga Bauchi domin jin karin bayani:


Like it? Share with your friends!

0

You may also like