Shugaban kasar Masar ya bayyana cewa babu wata kasa da ta kafa sansanin Soja a cikin kasar
A yayin firarsa da Jaridar Misri, Shugaban Kasar Masar Abdulfatah Alse-se ya karyata jita-jitan cewa a kwai Sansanin Sojan Rasha a arewa maso gabashin kasar sannan ya ce a halin yanzu babu wata kasa daga cikin har da Rasha da ta kafa sansanin Soja a cikin kasar kuma ko nan gaba Gwamnati ba za ta bayar da dama ga wata kasa ta kafa sansanin Sojojinta a cikin kasar ba.
A yayin da yake magana kan alakar kasar da Rasha, Alsese ya ce domin samun daidaito a siyasar kasa da kasa wajibi ne Masar ta kyautata alakar ta da kasar Rasha.
A yayin da yake bayyani kan alakar kasar sa da kasashen Larabawa, Shugaba Alse-se ya kara da cewa Masar gungu ceĀ a kungiyar kasashen Larabawa kuma ta nada kyakkyawar alaka da dukkanin kasashen Larabawa.