Hukumomi a kasar Masar sun toshe dukkan asusu da kaddarori na kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda biyar da wasu kungiyoyin fararen hula uku, al’amarin da ke sa zullumin watakila Gwamnatin ta kaddamar da yaki da kungiyoyi kare hakkin bil’adama gadan-gadan.
Hukumomin kasar na ta binciken irin wadannan kungiyoyi da ake zargin suna wuce gona da iri da zargin suna samun makudan kudade daga kasashen duniya domin haifar da rudani a cikin kasar.
Tun a shekara ta 2011 aka fara wannan takun saka da kungiyoyin kare hakkin bil’adama, a lokacin da hukumomin Masar suka ce kungiyoyin kare hakkin bil’adama da ke kasar ke ta kokarin haddasa fitina tsakanin kasar da Amurka.