Masari Ya Nemi Masu Zuba Jari A Harkar Hako Ma’adanai Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari,  yace binciken da hukumar cigaban ma’adanai ta kasa ta gudanar yayi nuni da cewa Allah ya albarkaci jihar da ma’adanai  35,wadanda suke bukatar a fara Hakosu.

Masari wanda yayi magana ta bakin mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu,a taron masu hakar ma’adanai, ya tabbatar da shirin gwamnati na hada gwiwa da kowane dake da shaawar harkar hako ma’adanai a jihar.

Masari ya shawarci masu ruwa da tsaki da su taimakawa yinkurin gwamnati na bunkasa bangaren hako ma’adanan karkashin kasa, saboda faduwar farashin mai, yasa dole gwamnati ta nemo wasu hanyoyi da zata samu kudaden shiga.  

Gwamnan yayi umarni da asamar da hanyar biyan kudi guda daya tilo na dukkanin kudin da jihar ke samu daga bangaren ma’adanai, domin kaucewa biyan haraji sau biyu da, inda yace yinkurin wani bangare ne na bin dokar ma’adanai da gwamnatin jihar ta samar a shekarar 2007. 

You may also like