Masari ya sallami kwamishiniyar ilimi ta jihar KatsinaGwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sauke kwamishiniyar ilimi ta jihar,Farfesa Halimatu Idris daga kan mukaminta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin yada labarai Alhaji Abdu Labaran ya fitar.

Sanarwar ta rawaito wata wasika da gwamnan ya sanyawa hannu  inda yake godewa Farfesar kan gundunmawar da ta bayar  wajen cigaban ilimi a jihar.

 “Lokacin da take matsayin kwamishinan ilimi a jihar an gyara makarantu da dama aka  daga darajar wasu kana aka gina wasu sababbi tare da samar da yanayin koyo da koyarwa  mai kyau. 

“Amma kuma yayin da al’amuran zaben shekarar 2019 ke shirin farawa ya zama lallai kan gwamnati da ta shigo da sababbin jini yan siyasa da za su taimakawa aiyukan gwamnati,” Masari ya ce.

You may also like