
Haɗarin ya afku ne a lokacin wani bukin a Calabar babban birnin jihar Cross Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, lamarin da ya janyo rasuwar mutane 14 tare raunata wasu mutum 24.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Cross Rivers, SP Irene Ugbo , ya sanar da BBC cewar su na ci gaba da yunƙuri ceto rayukan waɗanda haɗari ya rutsa da su.
Haɗarin ya faru ne a ranar Talata a lokacin bukin wasa da babura da aka gudanar a titin Mary Slessor a Bogobiri, daya daga cikin manyan hanoyoyi da aka tanada na wasan na bana.
Wani ganau ya ce babur din ya ƙwace wa matuƙin da ke gudun wuce sa’a, wanda hakan ya sa ya kutsa cikin ‘yan kallo.
“Da alama matuƙin da babur din ya ƙwace mawa, ya kutsa cikin mutane ne, ya kuma buge mutanen da ke kallon bukin wasa da baburan,” a cewar ‘yan sandan.
SP Ugbo ya ce “wadanda ake zargi na hannunsu bayan faruwar lamarin”.
Gwamnan jihar Cross Rivers Farfesa Ben Ayade, ya soke bukin, inda ya buƙaci da a gaggauta kaddamar da bincike kan faruwar mummun lamarin.
A wata sanarwa da daraktar yaɗa labaru ta gwamnan jihar, Christian Ita, ta ce “gwamnan jihar na son sanin yadda matuƙin babur ɗin ya sami damar kutsawa inda ake bukin, duk da an rufe hanyar ga mutanen gari”.
SP Ugbo ya ce ‘yan sanda sun maido da zaman lafiya bayan faruwar lamarin.
A wasu hotunan bidiyo masu tayar da hankali da ke yawo a kafafafen sada zumunta, sun nuna munanan ranunkan da wanda haɗarin ya rutsa da su suka samu.
Bukin hawa babura na daya daga cikin manyan wasannin kalakuwa da ake yi a birnin na Calaba, a jiha wadda ta yi fice wajen shirya irin wadannan bukukuwa.
Gwamnatin Jihar ta Cross Rivers ce dai kan dauki nauyin bukin, da ake gudanarwa shekara-shekara, wanda hakan ya sanya ya zama daya daga cikin bukukuwa da ke jan hankula a Najeriya a ƙarshen kowace shekara.
An fara gudanar da bukin a 2004 a matsayin wasan janyo hankulan masu yawan buɗe ido a birnin Calabar.
A yayin bukin matuƙa baburan kan gudanar da nau’ukan wasanin da babur iri-iri, domin ƙayatar da masu kallo.
A duk lokacin da ake gudanar da bukin, akan taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a hanyoyin da aka shirya cewa masu wasa da baburan za su bi.