Mashayin direba ya kashe yara 5 a jihar Akwa Ibom


A ranar lahadi wani mashayin direba ya kashe yara 5 har lahira a yankin Ukana Ikot Etim dake karamar hukumar Essien Udim ta jihar Akwa Ibom.

Mutumin yana tuka motar kirar kamfanin Ford mai dauke  da rijistar namba  GCE 342 CX, hadarin dai yafaru ne lokacin da direban yayi  kokarin kaucewa yara 2 akan hanyarsa, yayin da motar tayi awon gaba da yara bakwai dake kan mahadar hanyar Ukana Ikot Etim.

Godwin Anthony wanda abun yafaru a idon sa ya shaidawa jaridar punch cewa biyar daga cikin yara sun mutu nan take yayin da aka garzaya da 2 zuwa  asibiti.

Lokacin da mutane suka isa wurin sun iske direban cikin mayen giya, yanzu haka dai direban na hannun jami’an yan sanda.

 

 

You may also like