Wani masinja mai suna,Malam Abubakar Shuaibu dake da shekaru 45 wanda ke aiki a makarantar sakandaren gwamnati ta Aminu Marmara dake Sabongari Zariya,jihar Kaduna a ranar Talata ya yanke jiki ya fadi bayan da ya karbi takardar sallamarsa daga aiki.
Wata majiya da ta sheda abinda yafaru ta fadawa kamfanin dillancin Labaran Najeriya afkuwar lamarin.
Majiyar tace lamarin ya faru da safiyar ranar Talata lokacin kaɗan bayan mutumin da abin ya shafa ya karbi takardar sallamarsa daga aiki.
Yace masinjan ya yi wa gwamnatin jihar aiki har tsawon shekaru 11.
“Munje aiki da safiyar yau shi kuma Abubakar Shuaibu an gayyace shi zuwa ofishin ilimi na shiya yana isa wurin suka mika masa takardar sallama daga aiki.
“Da ya dawo makaranta ya nuna takardar mun ba shi shawarar ya dauki haka a matsayin ƙaddara daga Allah da saboda babu abin da zai samu mutum face Allah ya ƙaddara faruwar hakan.
“Ya kuma amince cewa haka Allah ya ƙaddara masa, amma kawai sai ya fadi sumamme.
“Mun bashi taimakon gaggawa da sauri inda muka ɗauke shi muka kwantar da shi a kasa tare da yi masa fifita kafin ya fara farfadowa a hankali cikin hayyacinsa.”ya ce .
Majiyar ta NAN ta kara da cewa malaman makarantar dake wurin sun haɗu inda suka cimma matsayar tara masa kudi daga albashinsu.
Idan za a iya tunawa gwamna Nasir El-Rufai ya bada umarnin a kori duk wasu masinjoji, masu goge-goge da kuma direbobi da suka shafe shekaru 10 a bakin aiki kuma basu da matakin ilimin Difiloma ko NCE .