Masu barazanar hana zabe, cika baki ne kawai – Buratai Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai

Asalin hoton, OTHER

Tsohon Babban hafsan sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya bayyana kwarin gwiwa game da zaben Najeriya da za a fara a cikin watan Fabrairun 2023.

Janar Buratai, wanda dan kwamitin yakin neman zaben Cif Bola Ahmed Tinubu, ne na APC a zaben, yayin wata ziyara a sashen Hausa na BBC, ya ce yawancin masu barazanar hana zabe, magana ce kawai ta fatar baki , ba da gaske suke yi ba.

Ya ce, ‘’ Ni a ganina barazana kawai suke, domin sojojin Najeriya da ‘yan sanda da ma sauran jami’an tsaro sun daura damarar tunkarar duk wanda zai tayar da wani hargitsi a lokacin zabe.”

Laftanar Janar Tukur Yusuf Burutai, ya ce akwai fargaba da koke koken da ake, a kan cewa za a iya samun matsala a lokacin zaben mai zuwa, to yakamata mutane su duba su gani a yanzu akwai ci gaba wajen tabbatar da tsaro a Najeriya, bisa la’akari da shekarun baya da aka yi zabe.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like