Masu Canza Sheka Daga PDP Zuwa APC  Sunayi Ne Dan kar Gwamnati Ta Kama Su – Sule Lamido



Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya danganta cenja Shekar da wasu keyi daga jam’iyar adawa ta PDP zuwa Jam’iya mai Mulki APC da jin tsoron kamun da gwamnati keyi.
Sule Lamido wanda ya yi magana da manema labarai a gidansa dake Bamaina yace, duk wani wanda ke son samun walwala to ya zama dole ya cenja sheka ya koma APC.
Sule Lamido yace, duk gwamnatin da ta dauki hanyar danniya da nuna wariya kamar yanda hakan ke faruwa a yanzu to babu shakka wannan gwamnati zata kasa aiwatarda komai a mulkinta.
Sule Lamido ya bayyana fitar da wasu ‘yan Jam’iyar PDP keyi zuwa APC a matsayin jin tsoron wulakanci.
“Idan aka rasa samun adalci, Idan kuna da gwamnatin da bata son gaskiya, to dole ne mutane su nemi mafaka, don haka wadanda ke fita daga jam’iyar PDP zuwa APC suna neman mafaka ne.”
“Wannan gwamnati da ke ci yanzu ba za ta taba iya yin ayukka ba, duk yadda mutane ke sonta, duk yanda mutane ke mata addu’a, ba zata yi ayukka ba saboda bata da karfin daukar Nijeriya” a cewar Sule Lamido.

You may also like