Masu Damfarar Majinyata A Kano Sun Shiga Hannu


 

 

Sakamakon korafi da wasu majinyata da makusantan abisitin kwarraru na Murtala Muhammad da ke Kano suka yi a kan saba ka’idar karar kudaden aiki a hannusu, yanzu haka hukumar gudanarwar asibitin ta sha alwashin daukar mataki kan lamarin.

Shugaban asibitin, Dakta Nura Idirs wanda ya bayyana haka ya ce majinyatan sun yi zargin cewa abubuwan da ke faruwa a wajen gwaje-gwajen jini da ake kira ‘R.B.S’ da ‘FBC’ da ‘PCB’ da sauransu a asibitin, ana karbar kudin mutane ba tare da an ba su rasiti ba kuma ana kara musu kudi wanda suka yi zargin cewa kudin ba ya shiga aljihun gwamnati. Don haka suka shawarci hukumar gudanarwa ta asibitin ta dau mataki na dakile wannan harka da ta saba ka’ida.

Dakta Nura Idris ya bayyana cewa ba shakka wanna korafi sun same shi don haka yanzu sun dau mataki na zabari da nemo bata-gari da ke wannan cuwa-cuwa ko cin hanci da rashawa a asibitin na Murtala don hukunta su daidai da manufar gwamnatin Kano da ta kasa a kan yaki da cinhanic da rashawa a kowanne mataki.

Haka kuma Dakta Nura ya ce a baya ma an sami makamancin irin wannan abu ta yadda wasu ‘yan kasuwa da ke bakin asibiti suka rika shiga harkar da ba tasu ba ta hanyar cuwa-cuwar kati da su ke samu daga wasu baragurbin ma’aikata suna sayar wa masu son ganin likita a asibitin.

Ya bayyana cewa a lokacin da wannan korafin ya zo kunnensu, nan da nan suka dau mataki na kafa kwamitin binciko masu wanna laifi wanda aka gano su tare da hukunta su, kana na wajen asibitin aka hada su da jami’an tsaro don kai su gaban shari’a.

“Don haka hukumar asibitin Murtala za ta cigaba da yin aiki ba-sani-ba-sabo a kan duk wanda aka kama yana yin wani abu da ya saba ka’idar aiki. A bangarenmu kuma, za mu ci gaba da yin aiki na taimaka wa marasa lafiya bisa gaskiya da rikon amana, tausayi da sanin ya kamata.” In ji shi.

You may also like