Wasu mutane 10,masu Fafutukar tabbatar da kasar Biyafara sun kai babban hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai kara gaban wata kotu dake kasar Amurika.
Masu gabatar da kara sun zargi Buratai da kuma wasu mutane 13 da hannu wajen ganawa masu fafutukar tabbatar da kasar Biyafara azaba da kuma aikata kisan kai.
Masu karar suna son abiyasu diyar miliyoyin daloli na wahalar da suka sha da kuma asarar rayukan yan uwansu da sukayi.
A wani taron manema labarai da suka gudanar a Jihar Legas, wasu kungiyoyin fararen hula sunyi zargin cewa anaso ayi amfani da masu karar ne domin a sanyaya jami’an tsaro gwiwa a yunkurin da suke na tabbatar da tsaro a kasarnan.