Masu Garkuwa Da Mataimakin Kwamishinan Yan Sanda Sun Bukaci Kudin Fansa Naira Miliyan 50  


Yan bindigar da suka sace mataimakin kwamishinan yan sanda, Emmanuel Agene sun tuntubi rundunar yan sanda dake Gusau inda suka bukaci miliyan 50 a matsayin kudin fansa wata majiya dake hedikwatar rundunar yan dake Gusau ta shaidawa jarida Daily Trust cewa masu garkuwa da mutanen sun bayyana hakane a ranar Alhamis. 

Yace yan bindigar sun nemi a basu kudin kafin su sako jami’in dan sandan. 

ACP Emmanuel Agene, an sace shi ranar Laraba akan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua akan hanyarsa ta komawa wurin aiki.

Rundunar yan sandan jihar Zamfara taki yarda tayi magana akan batun, kuma baza ta iya tabbatar da bukatar biyan diyar ba, amma majiyar tace har yanzu ana cigaba da tattaunawa. 

Amma rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sace mataimakin kwamishinan. 

Mai magana da yawun rundunar ASP Mukhtar Hussein Aliyu yace mataimakin kwamishinan na kan hanyarsa ta komawa Zamfara tare da direbansa lokacin da aka sace shi. 

You may also like