‘Masu garkuwa da mutane na yanka mana haraji a wani yanki na Zamfara’A Jihar Zamfarar Najeriya, mutum huɗu sun mutu wasu goma sun samu raunuka a garin Ruwan Baure da ke cikin karamar hukamar Gusau bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yammacin Litinin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu garkuwa da mutanen suka sako wasu mutane sama da 200, sai dai sun kashe wasu mutum 28 a lokacin da suka yi garkuwar da su a garin Randa da ke cikin karamar hukumar Maru a Jihar ta Zamfara.

‘Yan bindigan sun kai hari zuwa garin Ruwan Baure ne da misalin karfe 6 na maraicen Litinin.

Wannan mutumin da BBC ta sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya shaida harin da aka kai, kuma ya ce da kyar ya tsira da ransa.


“Maharan sun afko wa garin bisa mashin kusan 100.”

Ya ce an dauko gawarwakin mamatan kuma ana shirin yi musu sutura, kuma rikicin ya sa wasuna kauracewa yankin.

“Ga mata can da yara suna takawa a kafa zuwa kasar Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu. Maza ne kawai suka tsaya a garin domin a yi wa mamatan jana’iza.”

Ya koka kan rashin daukar mataki daga bangaren hukumomin jihar.

“Mutanen nan an san inda suke, an san uwayensu domin ba baki ba ne. har ta kai ga ranar talata sun yanka wa mutanen Gora tara ta Naira miliyan biyu, kuma sun je garin da motar daukan kaya samfurin Canter kuma suka raba mazauna garin da buhu 130 na dawa.”

‘Yan bindiga sun sako mutum 200 da suka yi garkuwa da su a garin Randa

Wannan mutumin na cikin wadanda aka sace:

“Mu 162 aka dauka daga garinmu, kuma kwananmu 20 daidai a hannunsu, sai ranar Lahadi suka sako mu.”

Ya ce masu garkuwa da su sun raba su cikin dakuna shida, kuma babu wanda ya san ainihin abin da ke faruwa, sai dai abin da aka gaya musu.

“Cikin wadanda aka sace tare da ni, mutum 28 ‘yan bindigar suka kashe. Ko da yake wasunsu yunwa da wahala ce ta yi sanadin mutuwarsu.”

Amma ya ce wadanda wuya ta sa suka mutu ba su wuce mutum uku ba, “sauran harbe su aka yi.”

BBC ta tuntui rundunar ‘yan sandan Najeriya a Jihar ta Zamfara, sai dai kakakin rundunar ya ce jami’ansu na kan bincike kan wannan lamarin.


Shi ma ya koka ganin yadda barayin dajin ke kai musu hari a duk lokacin da suka ga dama.

“Tun da farko mun ba su miliyan shida, amma sun ce suna bukatar mu tara musu karin miliyan 30 ne. Sannan kafin wannan lokaci sun sace mana buhunan dawa fiye da 200.”Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like