Wasu masu garkuwa da mutane wadanda suka samu nasarar sace Shugaban PDP na jihar Filato, Damishi Sanga sun nemi a biya Naira milyan 100 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban PDP wanda ya taba rike mukamin Ministan Wasanni, an sace shi ne a kan hanyarsa ta zuwa Abuja shi da direbansa da kuma wani dansa.