Masu Garkuwa Da Mutane Sun Kashe Wani Dan Kasuwa Suka Kuma Sace Matarsa Akan Hanyar Abuja-Kaduna


Masu garkuwa da mutane sun kashe wani matafiyi kana sukayi garkuwa da maidakinsa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi.

Wata mata dake da kusanci da iyalan marigayin tace ma’auratan na kan hanyarsu ta zuwa Abuja lokacin da motar da suke ciki  ta lalace. 

“Masu garkuwa da mutanen sun kashe Sharif a gurin nan take kana suka yi awon gaba da maidakinsa zuwa maboyarsu dake cikin Daji,” a cewar matar. 

Tun farko dai sun bukaci kudin fansa naira miliyan 20 kafin su saki matar marigayin  amma daga bisani suka rage kudin zuwa miliyan 10.

“Bazan iya fadar kudin fansar  da aka biya ba amma an sako ta ranar Litinin bayan da aka biya miliyoyin kudade,” tace. 

Marigayi Sharif ya mutu ne dai-dai lokacin da suke bikin cika shekaru 6 da aure. 

 

You may also like