Rundunar ‘yan sandan jahar Lagos ta bazama neman wasu ‘yan makaranta da malami daya da shugaban makaranta wadanda masu garkuwa da mutane suka sace a cikin harabar makarantar a safiyar yau Alhamis.
Rahotanni sun nuna cewa yara guda biyu a cikin hudun da aka sace sun kubuta, inda ‘yan sanda ke neman sauran biyun da kuma malaman.
‘Yan bindigan sun farwa makarantar mai suna Government Model Secondary schoool da ke Igbonla, Epe yayin da yaran ke addua a filin taron makaranta, inda suka kwashi yaran, suka kuma yi awan gaba da shigaban makarantar da malami daya.
Tuni majalisar jahar ta yi kira da hukumomin tsaro da su karfafa binciken da suke yi domin ganin an samu yaran cikin gaggawa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar, Bisi Kolowale ya bayyana cewa suna nan su na iya kokarinsu kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai mutanen sun fito.