A garin Jere dake Jahar Kaduna jami’an tsaro sun yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane domin neman fansa su 19 wadanda suka addabi hanyar Abuja zuwa kaduna da Kano
Haka kuma wadanda akayi nasarar chafkewar sun hada da masu sayarda makamai da albarusai na bindigar AK 47 dama kayan damarar sarki da jami’an tsaro
Andai gabatar da wadannan yan ta’addar ne gaban yan jaridu inda mai hulda da manema labarai na hukumar Yan sandar wato CSP Jimoh Moshood ya jagoranta a garin jeren dake jahar ta kaduna
Haka kuma hukumar ta jami’an tsaro tayi nasarar kwace wasu bindigogi kirar AK47 guda 8, hadi da wasu bindigogin da dama kirar gida da kuma kayin sarki na jami’an tsaron
Jinjina ga jami’an tsaron Najeriya
Jinjina ga shugaban yan sandar ta kasa wato IGP Ibrahim K. Idris
Jinjina ga jami’an tsaro na sirri