Masu Kada kuri’a 188,588 Suka Sanya Hannu Rijistar Yiwa Sanata Dino Melaye Kiranye. 


Mutane dubu dari da tamanin da takwas da dari biyar da tamanin da takwas (188,588) da suka fito daga mazabar Kogi ta yamma ,suka sanya hannu domin dawo da Sanata Dino Melaye, wakilinsu a majalisar dattawa gida. 

Yunkurin Dawo da Sanatan gida yafara ne makonni biyu da suka gabata a kananan hukumomi bakwai da suke  a mazabar Kogi Ta Yamma. 

Tuni Sanata Melaye ya zargi gwamna Yahaya Bello da hannu a yunkurin dawo dashi gida daga majalisar, zargin da Bello yasha musaltawa.

Jami’in tattara sakamakon zaben kiranyen, Malam Adamu Yusuf,  da yake bayyana sakamakon zaben daga kananan hukumomi bakwai,yace an tattara sakamakon ne a ranar Asabar a garin Kabba.

Mallam Yusuf yace jumullar mutane masu kada kuria a mazabar sune 360,098 ,yayin da mutane 188,588 suka sanya hannu a rijistar dawo da Sanatan. 

“A karkashin tsarin mulki ana bukatar kaso 51.1 cikin dari na masu kada kuria, kuma tuni muna da kaso 52 cikin dari,”yace. 

You may also like