Masu kanjamau sun rasa kulawa a Najeriya


gettyimages-sida1200_0

 

Gidauniyar kula da masu cutar kanjamau a Najeriya ta bayyana cewa, kimanin mutane miliyan 3 da dubu 400 ne ke dauke da cutar a kasar.

Sai dai mutane dubu 700 ne kawai daga cikinsu ke samun kulawa da kuma shan magani, kamar yadda manajan gidauniyar, Adetayo Towolabi ya sanar a yau jumma’a a birnin Abuja.

Mr. Towolabi ya nuna damuwarsa kan alkaluman masu fama da cutar a cikin kasar mai yawan mutane miliyan 170, wadda kuma ita ce ta biyu a Afrika bayan Afrika ta Kudu da ta fi yawan masu kanjamau.

Manajan ya ce, akwai yiwuwar nan gaba, adadin masu shan maganain za su ragu, sannan ya bayyana fargaban cewa, mutane miliyan 20 za su iya mutuwa shekarar 2030, matukar ba a mayar da hankali ba wajen kula da lafiyar masu cutar ta kanjamau ko kuma sida.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like