Dakta Boboye Oyeyemi shugaban hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta kasa FRSC ya ce ana ana shirin samar da wata doka da zata tilastawa masu amfani da ababen hawa biyan tarar ₦100,000 ga duk wanda aka samu da karya dokar tuki.
Oyeyemi ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a wurin taron tsara yadda za a kare faruwar haɗura a titunan Najeriya, ranar Laraba a Abuja.
“Baza ka kama mutum yana amsa waya lokacin da yake tsaka da tuki ba sannan ya biya tarar 4000 kana daga bisani ya koma ya cigaba da aikata laifin.
“Biyan kuɗin tara kamata yayi ya zama izina, shine yasa na ke goyon bayan abinda majalisar ƙasa take na gyaran dokar hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa domin ƙara yawan kuɗin tara da ake biya.
” Bani bane na kirkiro da wannan ba majalisar ƙasa ce ta kirkiri haka ina kuma goyon baya, zan tabbatar da cewa an zartar da kudurin ya zama doka kafin tsakiyar shekara mai zuwa.
“Ina da yakinin cewa idan masu karya dokar titi suka fara biyan tara mai yawa tsakanin ₦50,000 zuwa ₦100,000 kan aikata laifi ɗaya baza su so aikata laifi irin haka ba anan gaba.”