A Najeriya ɗalibai makafi na ƙorafi kan rishin koyar da darussan lissafi a wasu makarantu wanda hakan ke zama kalubale a gare su wajen samun illimi mai zurfi a kasar.
Sanadiyar hakan ne aka gudanar da wata tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi da kuma shugabanin kungiyar makafi ta Najeriya domin lalubo bakin zaran.
Ishaq Adamu Gombe shi ne shugaban kungiyar makafi ta kasa a Najeriya, ga kuma karin bayanin da ya wa BBC game da abin da aka gano, da kuma shirin da ake yi domin magance matsalar.
“Yawancin masu lalurar gani kamar ni ba mu yi lissafi ba a makaranta, wannan ya biyo bayan kallon da ake yi mana ne cewa ba za mu iya lissafi ba.”
Ya ce a dokar Najeriya, “kafin a ba dalibi gurbin karatu a makarantun gaba da sakandare, sai yana da lissafi, amma hukumar ilimi ta rika ba mu ‘waiver’, wato ba a bukatar sai mun yi lissafi.”
Sai dai daga baya ya ce an sauya wannan bukata.
Wannan bukata na hana masu lalurara gani rasa damar zuwa manyan makarantun gaba da sakandare kamar jami’o’i, sannan yana yin tarnaki ga kokarin masu lalurar gani wajen samun ci gaba musamman a wajen aiki.
A kasashen duniya ana koyar da masu lalurar gani darasin lissafi, har ma a cikin wasu kasashen Afirka, inji shi.
“An bar mu a baya a Najeriya wajen wannan ci gaban na koyar da lissafi ga makafi.”
Ya kara da cewa an shirya wannan taron ne domin nemo hanyoyin magance wannan matsalar.
Ya ce akwai wata babbar matsala da ke hana masu lalurar gani yin lissafi.
“Yawancin makafi sun gaya wa kansu cewa ba za su iya lissafi ba baki dayansa.”
Wannan matsalar a cewarsa ta zama karfen kafa ga “kokarin da ake yi na ganar da makafi cewa za su iya koyon lissafi kamar kowa.”
Shi dai taron ya cimma matsay ta hada karfi da karfe wurin hada kan masu ruwa da tsaki a Najeriya domin samar da hanyoyin koyar da masu lalurar gani darussan lissafi a dukkan mataki na ilimi a fadin kasar.