Masu Shafukan Facebook na Bogi Su Shiga Taitayin Su – Bashir Ahmad


Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman akan sabbin kafofin sadarwa na  zamani wato Bashir Ahmad, ya yi bayanin cewa sun samu dangantaka mai karfi  da ma’aikatan Facebook, wanda hakan zai bada damar maganin masu bude “account din bogi suna cin mutuncin mutane . 
“Ka rubuta alkairi ka samu lada har bayan ka, ka kuma rubuta sharri ka mutu kabar shi a ci gaba da kai maka sakamako”.
Ya kuma jawo hankalin ma’abuta wannan kafa da su mayar da hankali gurin bada kariya akan bayanan karya da sharri da ka iya jawo rashin natsuwar matasanmu.
Alhaji Bashir ya yi wannan jawabi ne a zatawar da suka yi da ‘yan jaridu a gidan talabijin na jahar Katsina (KTTV) a cikin shiri na musamman.

You may also like