Masu Yiwa Kasa Hidima Zasu Maye Gurbin Likitoci Masu Yajin Aiki – Ministan Lafiya Ministan Kiwon Lafiya, Farfesa Issac Adewale ya bayar da umarni ga cibiyoyin lafiya na Gwamantin tarayya da ke fadin kasar nan kan su yi amfani da likitoci masu yi wa kasa hidima da ke cibiyoyin don maye gurbin likitoci da a halin yanzu suka fara yajin aiki.

Ya ce bin matakin ya zama dole don ganin marasa lafiya da ke cibiyoyin ba su shiga cikin yanayin kunci ba kuma hakan za ba gwamnati sukunin yin sulhu da kungiyar Likitocin a kan bukatunsu da suke neman a biya masu.

You may also like