
Asalin hoton, Getty Images
Rahotonni daga wasu jihohin kudancin Najeriya sun nuna cewa masu zanga-zanga sun cinna wuta a wasu bankunan kasuwanci a yankin, domin nuna adawa da tsarin babban bankin ƙasar kan sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar.
Ƙarin rahotonnin da muke samu sun nuna cewar an fasa wasu bankunan an kwashi ganima.
A birnin Benin babban birnin jihar Edo, masu zanga-zanga sun taru a kusa da reshen CBN da ke birnin, kafin daga bisani jami’an tsaro sun tarwatsa su ta hanyar amfani da borkonon tsohuwa.
Haka ma a Ibadan babban birnin jihar Oyo, masu zanga-zangar sun toshe wasu titunan birnin sakamakon ƙorafin ƙarancin takardun kuɗin.
Can ma a birnin Warri babbar cibiyar kasuwancin jihar Delta, masu zanga-zangar sun yi ɓarna a waɗansu bankunan kasuwanci.
Matakin na zuwa ne bayan da kotun ƙolin ƙasar ta ɗage sauraron ƙarar da wasu jihohin ƙasar suka shigar gabanta suna neman ƙara wa’adin amfani sofaffin kuɗin ƙasar.
Abin da kotun ƙoli ta ce kan wa’adin naira
Kotun Ƙolin Najeriya ta ɗage zaman sauraren shari’ar da wasu gwamnonin jihohin ƙasar suka shigar kan ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar na takardar naira 200 da 500 da 1,000.
Kotun Ƙolin Najeriya dai ta ɗage zaman bayan da wasu jihohi guda tara suka bi sahun gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara waɗanda suka shigar da ƙarar tun da farko.
Jihohin da ke ɓangaren masu ƙarar bayan guda ukun na farko su ne Kano da Katsina da Sokoto da Lagos da Ondo da Ogun da Ekiti da Rivers.
Ita ma a ɓangarenta gwamnatin tarayyar ƙasar ta samu jihohin Edo da Bayelsa a matsayin waɗanda ke mara mata baya a shari’ar.
Yanzu dai al’ummar Najeriya za su ci gaba da jira har zuwa 22 ga watan Na Fabrairu kafin sanin matsaya game da ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin ko kuma a’a