Masu Zanga Zanga Sun Kona Kamfanin Siminti Na Dangote


 

 

Gwamnatin kasar Habasha (Ethiopia) ta sanar da cewa masu zanga-zanga a kasar sun kona motoci da wasu kayan aiki a kamfanin siminti na Aliko Dangote da ke yankin Oromia a kasar.

Masu zanga zangar sun fito ne domin su nuna rashin jin dadinsu game da mutuwar akalla mutane 55 a wani turmutsitsin da aka yi a wajen bikin addinin na kabilar Oromo da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata, da kuma jikkatan mutane da dama.

Masu zanga zangar sun koka da yadda dakarun tsaron kasar su ka bude wuta kan masu bikin addinin a sakamakon yin wata wakar bukatar neman ‘yancin siyasa da suka yi.

Yayin zanga zangar ne, mutane suka afkawa motoci da kayan aikin kamfanin, suka cinna masu wuta.

Haka kuma sun kona wani caji ofis, da kotu da motar gwamnati, sun kuma saki wasu fursunoni a yayin zanga-zangar.

Hoto daga: Zehabesha.com

Like it? Share with your friends!

0

You may also like