Masu zanga-zanga sun rufe wata babbar hanya a Abuja 


Manyan motocin ɗaukar kaya da kuma matafiya aka tilastawa tsayawa na tsawon sa’o’i yayin da mazauna kauyen Tungar Maje dake karamar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja, suka gudanar da zanga-zanga kan zargin da suke cewa rundunar sojan Najeriya na shirin rabasu da gonakinsu.

Gonakin da aka ce sun fara daga mahadar Giri dake kan hanyar zuwa filin jirgin sama na Abuja zuwa Zuba, tsawon sama da kilomita 44 kenan.

Al’ummar Koro da suka samu jagorancin Adamu Isiaku,sun shaidawa jaridar Daily Trust a wurin da ake gudanar da zanga-zangar cewa sun far gudanar da zanga-zangar ne bayan da suka lura cewa hukumomin sojoi sun kawo motocin hakan rami a ranar Litinin.

Sun dage cewa sojojin baza su karɓe musu kasarsu ta ainihi ba  kamar yadda suka yiwa wasu al’ummomi dake kan hanyar zuwa filin jirgin saman.

Sun ce kwamitin da gwamnati ta kafa makonni biyu da suka gabata har yanzu bai miƙa rahotonsa ba.

Zanga-zangar da ta gudana tun daga ƙarfe 7 na safiyar ranar Talata ta jawo wahala ga matafiya da kuma masu motoci dake ɗaukar dabbobi da kuma kayan abinci a tsakanin kudanci da arewacin ƙasarnan.

A karshe  yan sanda sun samu nasarar kawo karshen zanga-zangar da kusan misalin karfe 12 na rana.

You may also like