Mata a ƙasar Saudiyya za su fara shiga filayen wasan ƙwallon kafaMata a kasar Saudiyya yanzu haka sun sake samun wani yancin da abaya basu da shi.Daga shekara mai zuwa za a rinka kyale su shiga filin wasan kwallon kafa.

Hukumomin kasar ne suka bada wannan sanarwar a ranar Lahadi, a baya dai mazane kadai ke halartar filayen kallon wasan kwallon kafa.

Turki Al-Asheik, shugaban hukumar wasanni ta kasar ne yabada wannan sanarwa inda yace an yi hakan ne domin bunkasa bangaren wasanni.

Hakan dai ya yi dai-dai da burin da yarima mai jiran gadon sarautar kasar, Muhammad bin Salman yake dashi na kawo sauye-sauye a ƙasar.

Hukumomi za su fara gyaran manyan filayen wasan kasar dake biranen Jedda, Dammam, da kuma Riyadh domin su zama cikin shirin karbar iyalai mata daga shekarar 2018.

A watan da ya gabata dai a karon farko an gayyaci mata tare da iyalinsu zuwa filin wasanni domin halartar bikin ranar yan cin kasa a baya dai mazane kawai suke halartar irin wannan taron.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like