Mata da mijin ta sun gano kuskuransu dalilin yaudara ta da mijin yayi akan daukan fansa


am

Mu hadu da shi a ofishin na. kuma  ya kasance kyakyawan gaske,muka ci abinci tare har yake mu hirar.Yace sun rabo da matarsa ya kuma wajen mahaifiyarsa da zama,hirarmu tayi armashi har takaimu ga shakuwa da juna,abu kamar wasa sai muka fara soyaya.ya bani labarin abin da matarsa tayi

Yace matata tana da kishi sosai.kuma ni na bata wannan dama.takan daukimin waya tanamin bincike har wani lokacin takankira nambobin matan da ke wayar kuma yawancinsu abokan akina .tana cin mutuncin su .har takai na gaya mata bazan iya ci gaba da wannan halaiyarta ba.

Na yarda da zancen shi kuma na tausaya mai mutuka,muka fara soyaya mai zurfi.kwatam yace min zai dawo da matarsa.bayan kwana biyu,ina cikin bacci naji kira daga matarsa tana tambaya na dalilin dayasa nake soyaya damijinta.ranta a bace kuma da alamun kuka ma takeyi,nace mata bansan zancen datakeyi na.

Dasafe na kira shi ina tambayansa ya yaudareni .yace min

San da muke soyaya da matata,muna yawan fada har takai tafara son wani bayan ni.kuma gayan me kudi ne,yana da mota,wani sa in har ta gaban gidanmu suke wucewa rai na ya bacci mutuka,bayan su rabo na nemi auranta kuma ta amince amma ban taba manta abinda tayimin ba,shi yasa na nemi soyayarki don na rama abinda tayi min.

Daga karshe dai ashe matarsa tayi mai hakane don tasa shi kishi kuma ta jawo shi jikinta,amma a karshe ya kai ga azabtar da ita,ta kuma shaida masa yacce ya mai da ita babu kulawa ,babu kwanciyar hankali.Ya ganu laifinsa kuma yayi nadama mutuka.ya nemi gafarar matarsa,ya canja halayansa suka kuma zama lafiya da iyalansa.

 

You may also like