Ranar juma’a ta kasance rana mai tarihi a ƙasar Saudiyya yayin da akaran farko aka kyale mata magoya bayan ƙungiyoyin kwallon kafar kasar shiga filayen wasanni.
An kyale mata su shiga filayen wasannin kwallon kafa karon farko a tarihin ƙasar ta Saudiyya.
Wasan na ranar Juma’a an kara ne tsakanin kungiyar Al-Ahly da kuma Al-Batin a gasar cin kofin kwararrun ƙungiyoyin ƙwallon kafar kasar a filin wasa na Sarki Abdullah dake Jidda.
Cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata ne aka cimma matsayar bawa mata damar shiga filayen wasannin kafa a ƙasar.
Matakin na daga cikin sauye-sauyen da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ke samarwa a kasar.