Mata ‘Yan Kunar Bakin Wake Sun Mutu A Jihar Borno 



Wasu mata uku maharan kunar bakin wake sun rasa rayukanu bayan daya daga cikinsu ta tada bam din da ke jikinta a kusa da wasu tankokin mai a safiyar yau a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Tankokin man guda biyu da aka ajiye su akan hanyar Damboa, sun kone kurmus sakamakon aukuwar lamarin.
Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa a yankin arewa maso gabas, Abdulkadir Ibrahim, ya ce, tuni aka kwashe gawarwakin maharan na kunar bakin wake.
Ibrahim ya ce, an kuma shawo kan gobarar da tashin bam din ya haddasa, yayin da wasu majiyoyi ke cewa, harin bai shafi  jama’a ba.

You may also like