Bangaren mata na kungiyar yan uwa musulmi da akafi sani da shi’a sun gudanar da zanga-zangar neman a saki shugaban kungiyar Ibrahim El-zakazky wanda ke tsare a hannun jam’ian tsaro tare da mai dakinsa.
Zanga-zangar ta gudana ne a ofishin hukumar kare Hakkin Dan Adam Ta Kasa.
Masu zanga-zangar sun zargi gwamnati da kin bin umarnin hukuncin da kotuna suka yanke na a saki shugaban kungiyar.
Sai dai gwamnatin tace tana cigaba da tsare shugaban kungiyar ta shi’a ne domin tsaron lafiyarsa.
Kungiyoyin kare hakkin bil-adama da dama sun sha kiraye-kirayen gwamnati ta sake shi amma tayi kunnen uwar shegu da kiran nasu.
Abin jira a gani shine ko yaushe shugaban kungiyar ta yan uwa musulmi zai shaki iskar yanci.