Gwwmnan ya kayyade matakai uku da Gwamnatinsa ke dauka domin kawo karshen rikici da kashe kashen da yaki ci yaki cinyewa a Kudancin jihar.
A jawabinsa yayin da ya karbi bakuncin majalisar Sarakunan jihar a karkashin jagorancin Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, Gwamnan ya bayyana cewa mataki na farko da ya dauka shine na ganawa da shugaban hafsan soji domin neman a girke bataliyar sojoji Biyu a yankin, daya a Kachia daya kuma a Kafanchan.
Yace za a ginawa sojojin bariki a yankunan da zasu zauna domin tabbatar da tsaro,
Sauran matakan sun hada da kamo wadanda suke da hannu a tada rikicin da kashe kashen sannan a gurfanar dasu a gaban shari’a domin hukuntasu.
Sai kuma batun zaman sulhu da duka bangaririn, kuma tuni ya gayyaci cibiyar wanzar da zaman lafiya da ta jagoranci sulhunta rikicin jihar Plateau da su zo kudancin Kaduna su shiga tsakani a tattauna da duka bangarori domin nemo mafita ta karshe a kai.
Gwamna El-rufai ya kuma sake jaddada cewa shi da mataimakinsa da sauran mukarrabansa sun rantse da Al’kurani da Bibile gabanin fara aiki da nufin za su yi aiki tsakaninsu da Ubangiji ba tare da nuna fifiko ko son kai ba, yana mai cewa akan haka suke jagorantar jihar tsakani da Allah ba tare da nuna fifiko akan kowane bangare ko nuna wariya ba.
A cewarsa ko wajen bayar da ayyuka da yake yi yana kwatanta adalci a duka bangarorin domin rike amanar aiki.
“Kowannenku yaga yadda ake fancama ayyukan cigaba da raya kasa a gundumominsa ba dare ba rana” inji Gwamnan.
Tun da farko Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris wanda ya jagoranci tawagar ya ce sun yi Allah wadai da kashe-kashen da ake yi a kudancin Kaduna tare da yin kira ga hukumomin tsaro su tashi tsaye domin yi wa tufkar hanci.