
Asalin hoton, INEC
Hukumar Zaɓe mai zaman Kanta a Najeriya INEC ta bayyana matakan da za a bi domin kaɗa ƙuri’a a ranar zaɓe.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta bayyana matakai bakwai da ta ce za a bi domin kaɗa ƙuri’a ranar zaɓen.
A ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun dokokin ƙasar.
Matakin farko shi ne lokacin fara zaɓen wanda hukumar ta ce zai fara da misalin ƙarfe 8:30 na safe.
Mataki na biyu shi ne gabatar da katin zaɓe ga jami’an zaɓe domin tantance shi ta hanyar amfani da na’urar BVAS.
Daga nan sai a duba ko sunan mutum na cikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a a wannan rumfar zaɓen.
Mataki na gaba shi ne na’urar BVAS za ta tantance mutum ta hanyar saka ɗan yatsarsa a jikinta, daga nan sai a bai wa mutum ƙuri’ar da zai kaɗa.
Sai matakin kaɗa ƙuri’a wanda hukumar ta ce ta ware wuri na musamman da za a shiga domin kaɗa ƙuri’ar a asirce.
Matakin ƙarshe shi ne bayan kaɗa ƙuri’a mutum zai bar rumfar zaɓen, ko ya yi nesa da rumfar zaɓen na akalla mita 300.
A shirye muke domin gudanar da zaɓe
Hukumar zaɓen ta Najeriyar ta kuma ce a shirye take domin gudanar da babban zaɓen ƙasar kamar yadda aka tsara.
Duk da fargabar da wasu ƙungiyoyi da ɗaiɗaiku ke yi na cewa rashin tsaro na yin barazana ga babban zaɓen.
Shugaban Hukumar Zaɓen Farfesa Mahmood Yakub ya ce za a gudanar da zaɓukan kasar da ke tafe kamar yadda aka tsara a wannan shekara ta 2023.
Yayin da yake jawabi a taron majalisar zartarwar ƙasar da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a makon da ya gabata a fadar mulki da ke Abuja, Mahmood ya ce zaɓen zai gudana kamar yadda aka tsara.
Da yake zantawa da manema labarai bayan fitowa daga zauren majalisar, Farfesa Yakubu ya ce ya bayyana ne gaban majalisar ministocin domin sanar da ita irin shirin da hukumar ta yi na gudanar da manyan zaɓukan na bana.
Ya ƙara da cewa daman abin da aka saba yi ne a duk lokacin da ake daf da zaɓe a kasar, shugaban hukumar ya yi wa majalisar zartawa bayani inda shirye-shiryen suka kwana.
Haka kuma shugaban hukumar zaɓen ya sake bayyana gaban majalisar magabata ta ƙasa wato ‘Council of State’ ranar Juma’a.
Inda ya sanar da ita a hukumance irin yadda hukumarsa ta kintsa domin gudanar da manyan zabukan ƙasar.