Danna lasifikar da ke sama domin kallon hirar:
Dauda Ali Biu, muƙaddashin shugaban hukuma kiyaye aukuwar haɗura ta Najeriya, ya yi bayani game da tsare-tsaren hukumarsa game da yadda za su tunkari lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Ya ce hukumar ta fito da ƙarfinta da kayan aikinta ciki har da motoci da babura da motar bayar da taimakon gaggawa domin tunkarar wannan lokaci .
Ya ƙara da cewa hukumar na da jumullar ma’aikata dubu 25, tare da ma’aikatan sa-kai 11,000, waɗanda a cewarsa duka hukumar ta tura su kan titunan ƙasar domin kiyaye aukuwar haɗura a lokutan bukukuwan na Kirsimeti da sabuwar shekara.
Muƙaddashin shugaban hukumar ya kuma gargaɗi direbobi da su guje wa gudun wuce sa’a a kan titunan a lokutan bukukuwan, tare da kula da lafiyar ababen hawansu.