
A Indiya, ana girmar da ‘ya’ya mata na su zamo matan aure na gari da kuma uwaye sannan abu mafi muhimmanci a rayuwarsu kuma shi ne aure.
Sai dai, a yanzu mata da dama na da ra’ayin zama ba tare da aure ba wato zaman gwauranci.
A ranar Lahadi, na halarci taron cin abincin rana na mata 24 a wani shagon sayar da abinci na Caribbean da ke kudancin Delhi. Dakin ya cika makil, inda matan ke ta sowa da cacewa.
Dukkanin matan mambobi ne wata kungiyar gwagware – kungiya kuma da ke da shafi a dandalin Facebook na matan birni da basu da aure a India.
“Mu daina kiran kan mu da matan da suka rasa mazajen su ko wadanda aka sake ko zawarawa,’’ a cewar Sreemoyee Piu Kundu, wacce ta kirkiro da kungiyar, yayin Magana a wajen taron. ‘Kawai mu yi tinkaho cewa mu wadanda basu da aure ne.’’
Matan sun yi ta tafi da kuma nuna farin ciki.
Indiya dai ta ƙasance ƙasa da matan ta ke da burin yin aure, inda har yanzu ake nuna tsangwama ga wadanda basu yi aure ba.
A yankunan ƙarkara a Indiya, ana ganin mata gwagware na zama ɗawainiya ga ‘yan uwansu – damarmaki da matan da basu yi aure ba ke da shi ba ta da yawa sannan dubban zawarawa kuma ake kwashe su zuwa garuruwa masu sarki kamar Vrindavan da Varanasi.
Miss Kundu da sauran matan da na samu a wajen cin abincin su na daban ne. Yawanci sun fito ne daga gidajen da ke rufin asiri wanda ya hada da malamai da likitoci da lauyoyi da kwararru da ‘yan kasuwa da masu fafutuka da marubuta da kuma ‘yan jarida.
Wasu sun rabu da juna yayin da wasu kuma aurensu ya mutu ko zawarawa, inda wasu kuma basu ma taba aure ba.
Asalin hoton, Getty Images
Matan da basu da samari da ke zama cikin biranen da kuma ke da arziki, na ci gaba da jan hankalin mutane – kamar masu aiki a bankuna da masu yin ‘yan kunne da masu kamfanonin kasuwanci har ma da na tafiye-tafiye.
Matan da basu da samari na kuma samun karbuwa cikin al’adu – inda fina-finan Bollywood na Queen da Piku wadanda suka nuna matan da basu da samari na iya dogaro da kansu saboda suna da kudi.
A watan Oktoba, Kotun Kolin ƙasar ta yanke hukuncin cewa dukkanin mata wanda ya hada da wadanda basu yi aure ba, na da damar zub da ciki, abu kuma da matan da basu da samari suka ce abin a yaba ne domin kotun ta san da zamansu.
Sai dai duk da wadannan sauye-sauye, al’ummomi sun ki yin na’am da batun, inda miss Kundu ta ce zama ba tare da yin aure, ba abu ne mai sauki ba har ma ga wadanda ke da arziki, kuma ana yi musu mummunar fahimta a ko yaushe.
”Na fuskanci tsangwama da wulakanci a matsayina na mace mara aure. Lokacin da nake neman hayar gida a Mumbai, mambobin wasu gidaje sun yi mani tambayoyi kamar kina shaye-shaye? Kina yin jima’i?’’
Ta hadu da likitan mata wanda ya kasance kamar makwabci sannan shekaru kadan da suka wuce lokacin da mahaifiyarta ta saka talla a wani shafi a madadinta, ta hadu wani mutum wanda ya tambayeta ‘ko ita cikakkiyar budurwa ce a cikin mintuna 15 na farko’’?
“A gaskiya wannan tambaya ce da ake tambayar matan da basu da aure a ko da yaushe,” in ji miss Kundu.
Sai dai tsangwamar matan da basu da samari ko wadanda basu yi aure ba a Indiya abu ne da bai kamata a yi ba, saboda kidaya da aka yi a 2011, ya nuna cewa ana da matan da basu yi aure ba sama da miliyan 71.4 – alkaluma kuma da suka ɗara yawan al’ummomin Birtaniya ko Faransa.
Wannan ya ƙaru da kashi 39 – daga miliyan 51.2 da aka samu a 2001. An jinkirta yin kiɗayar 2021 saboda annobar korona, sai dai miss Kundu ta ce kawo yanzu, ‘yawan mu ya kai miliyan 100’’.
Ƙaruwar yawan matan da basu da aure ya faru ne saboda ƙara shekarun masu yin aure a Indiya. Alkaluman sun kuma hada na zawarawa saboda yawanci matan sun fi maza tsawon rayuwa.
Sai dai, miss Kundu ta ce tana ganin yawancin matan da basu da aure sune suka zabi haka.
“Na hadu da mata da yawa da suka ce su suka zabi zama ba tare da aure ba, sun ki yarda da batun aure saboda maza sun mamaye ko’ina wanda ba adalci bane ga matan.’’
Asalin hoton, SREEMOYEE PIU KUNDU
Mayar da hankali kan matan da basu da aure da Kundu ta yi – ya janyo wa mahaifiyarta wacce ta kasance bazawara a shekaru 29 tsangama.
“A lokacin tashiwa na, na ga yadda aka zamar da wata mata saniyar ware. Duk lokacin da halarci wani biki ko ma na auren ‘yan uwanta, basa ma ko so su ganta, inda ake fada mata cewa kada ta shiga lamuran amarya tun da ko kuruwar bazawara ba abu ne mai kyau ba ga amarya.’’
A lokacin da take shekara 44, lokacin da mahaifiyarta ta sake yin aure, miss Kundu ta zama abin magana cikin al’umma – ‘Me ya sa bazawara ta zama mace mai bakin ciki da shashanci da rashin jin dadi?
Ta ce tsangwamar da aka yi wa mahaifiyarta, ya shafeta matuka.
“Na girma da buƙatar ganin na yi aure. Na yi imani cewa aure zai kawo min karbuwa a cikin al’umma da kuma kore mani duhu.
Sai dai bayan rabuwa da samarinta har sau biyu wadanda kuma basu kare da da daɗi ba – da kuma bukatar ganin ta yi aure a shekaru 26, miss Kundu ta ce ta gano cewa auren gargajiya inda ake son mace ta yi wa mijinta biyayya, wannan ba nata bane.
Ta ce soyayya da ta yi, bai shafi al’adu ko addini ko ma al’umma ba, amma ta gina shi kan girmama wanda take so da mutuntawa juna.
Matan da basu da aure da na hadu da su a wurin cin abincin a ranar Lahadi, dukkansu sun yi na’am da hakan.
Sai dai, Indiya ta kasance al’umma da kashi 90 na aure da ake gudanar wa, ‘yan uwa ne ke shiryawa, inda mata basu da ta cewa kan wanda za su aura – balle kuma batun ko suna son aure ko a’a.
Amma Bhawana Dahiya, mai shekara 44, da ke da wata kungiya ta bayar da shawarwari kan soyayya kusa da Delhi, wanda kuma bai taɓa aure ba, ya ce abubuwa na sauyawa kuma ƙaruwar matan da basu da aure abin farin ciki ne.