
Asalin hoton, Family Photo
Wata uwa wadda ɗanta mai shekara 4 ya kusa mutuwa a Wales bayan haɗiyar ƙananan ƙwallayen ƙarfen magnet masu kama da ‘ya’yan carbi guda 52 da ke zuwa a jikin wani kayan wasan yara ta buƙaci iyaye su yi hattara.
Sai da likitoci suka cire wa yaron mai suna Jude ƙari, kuma suka yanka cikinsa har wuri biyar inda ƙwallayen ƙarfen suka maƙale.
Mahaifiyar Lyndsey Foley ta ce ta shiga fargabar cewa za ta rasa ɗanta Jude.
Hukumar kula da Lafiyar Al’umma ta Wales (PHW) ta buƙaci mutane su yi dogon tunani kafin su sayi duk wani nau’in kayan wasa mai ‘yan ƙananan ƙarafan magnet da baturin agogo don tsare lafiyar ‘ya’yansu.
Misis Foley, mai shekara 34, ta ce ta damu sosai bayan ɗanta, wanda yanzu ya kai shekara biyar, ya yi ta fama da rashin lafiya tsawon wata biyu a baya.
Bayan damuwar ta tsananta, a watan Agusta sai ta ɗauke shi zuwa asibitin Yarima Charles lokacin da cutar ta yi ƙamari.
Gwaje-gwajen jini da duba gangar jiki da likitoci suka yi wa yaron, duk sun nuna babu wani abu da ke damun Jude, kafin a yi hoton aksare (X-ray).
Asalin hoton, OTHERS
Ƙwallayen da Jude ya haɗiya sun yi kama da waɗannan a lokacin zafi
“Likita ya ɗauka cewa ko sarƙa ya haɗiya da farko, amma da na duba hoton, ni kawai na san cewa irin waɗannan ƙwallayen magnet ɗin ne,” in ji ta.
“Cikin minti biyar kuma sai likitoci suka shirya don motar ɗaukar marasa lafiya ta ɗauke su zuwa Asibitin Yara na Cardiff.
“Na yi ta fargaba. A lokacin ne kawai na fahimci irin matsanancin halin da muke ciki.”
Misis Foley ta ce ta sayi abin wasan yaran mai ɗauke da ƙwallayen carbi na ƙarfen magnet ne don ‘yarta Poppy mai shekara takwas.
Yara suna son irin wannan abin wasa, kuma akwai bidiyo iri-iri a dandalin Youtube da ke nuna yadda za a iya gina wasu surori ko siffofi da abubuwa ko gidajen wasan yara da su waɗannan ‘yan ƙananan ƙwallayen ƙarfen.
Mahaifiyar Jude ta ƙara da cewa: “Yana jin jiki. Abin tashin hankali ne. Na firgita sosai saboda ba zan iya ɗaukar ɗana na rungume shi ba, duk an sanya masa ƙananan bututun taimakawa yin numfashi.
“Na ma yi sa’a yaron ba shi da irin kwantacciyar cuta, amma duk da haka likitan fiɗa ya gargaɗe mu cewa mai yiwuwa sai an maƙala masa irin jakar da kashi zai riƙa taruwa tsawon rayuwarsa ko kuma a yi ta masa allurar bitamin duk wata saboda cikinsa motse.”
Yanzu dai Misis Foley na jan hankalin sauran iyaye game da hatsarin ‘yan ƙananan kayan wasan yara.
“Idan kana da irin waɗannan ‘yan ƙwallaye a gida, ku rabu da su, ya fi alheri. Suna da matuƙar hatsari.”Har yanzu ina jin tamkar laifina ne, idan na tuna halin da na jefa ɗana a ciki, ko kuma ka iya faruwa… Yadda rayuwarsa ta so canzawa saboda kawai na sayo masa abin wasan da nake tunanin yana da aminci. Ban taɓa tunanin illar da abin zai haddasa ba.”
Har yanzu ana kai Jude asibiti don a duba lafiyarsa kuma a tabbatar ba ya cikin hatsari, amma wani tabo mai tsawon inci biyar a cikinsa zai kasance wata hanyar tunawa da abin da ya faru.
Asalin hoton, SUPPLIED PHOTO/BBC
“Shi kansa Jude ya koyi darasi yanzu – kada ka riƙa jefa komai a bakinka,” in ji Misis Foley. “Kuma ni ma, kasancewata uwa, na ƙara sanin abin da ya fi dacewa na sayawa ‘ya’yana.”
Alison Farrar, ta kamfanin Trading Standards Wales, na cewa abu ne muhimmi a tabbatar cewa yara “ba sa wasa da kayan wasan da aka yi su, don yaran da suka ɗan fara girma”.
Kowanne abin wasa ana yin sa ne don yaran da ke cikin wani rukunin shekaru.
“kwai dokoki game da abin da ake sarrafa wasu kaya da su kuma irin waɗannan dokoki suna da tsauri idan abin da aka ƙera yana iya ɗaukar hankalin ƙaramin yaro – kai ko da abin ba a yi don wasan ƙananan yara ba,” cewar ta.
“Yara suna da ɗoki wajen bin abin da ake yayi musamman a shafukan sada zumunta, suna iya ganin bidiyon wasu yaran suna wasa da wani kayan wasa, amma abin da muke buƙata shi ne mu tabbatar cewa rukunin shekarunsu ya dace su yi wasa da irin wannan abin wasa.”To abin da ya faru kenan a nan shi yaron bai san cewa ƙwallon magnet yana da hatsari ba kuma iyayensa ba su san yana wasa da su ba.”
Sarah Jones, ƙwararriya kan fannin lafiyar muhallin al’umma a Hukumar kula da Lafiyar Al’umma ta Wales ta ce: “Muna neman iyaye su riƙa tunani cikin tsanaki kafin su sayi wani kayan wasa da ke ƙunshe da ƙwallayen magnet da baturan agogo ga yaransu.”Bai kamata a riƙa ajiye ‘yan ƙananan ƙwallayen magnet a inda ƙananan yara za su iya kai wa ba.”Akwai irin wannan hatsari idan yara suka haɗiyi batura agogo su ma.”