
Asalin hoton, Pushpa
Pushpa ta rubuta wa mutane sama da 1,000 jarrabawa
A shekarar 2007, wani makaho ya tambayi Pushpa da ta taimaka masa wajen tsallake titi. Bayan sun tsallake titin, ya sake neman wata buƙata da ya sauya rayuwarta.
“Ya tambaye ni ko zan iya rubuta wa abokinsa jarrabawa,” in ji Pusha
Ta amsa da cewa za ta iya, amma ranar da rubuta jarrabawar ta zo, murnar da Pushpa take yi ta ya koma ta fargaba.
Ba ta yi horon da ya kamata ba, kuma ba ta san me za a tambaya ba.
“Na kasance cikin sa’o’i uku na fargaba. Wanda na ke rubuta wa jarrabawar na faɗan amsar a hankali sannan da faɗa min cewa na yi ta karanta tambayoyin akai-akai,” in ji Pushpa wadda ke magana yayin da take zaune a wata kujera a garin Bengaluru da ke kudancin Indiya.
Sai dai ta yi iyakar kokarinta wajen taimaka wa Hema ƴar shekara 19 cin jarrabawarta.
Daga nan, Pushpa ta fara samun bukatar neman ta rubuta wa mutane jarrabawa daga wata kungiya mai zaman kanta da ke aiki da makafi, inda a cikin shekara 16 da suka wuce, ta zana wa mutum sama da 1,000 jarrabawa, duka kuma a kyauta.
“Ɗakunan rubuta jarrabawa sun kasance kamar gida a wajena,” in ji Pushpa yayin tattaunawa da BBC.
Kafa tarihin samun maki mai yawa
Baya ga rubuta jarrabawar makarantu da kuma ta jami’o’i, ta kuma taimaka wa mutane da ke zuwa rubuta jarrabawar da kuma gwaji da gwamnati ke yi na ɗaukar aiki.
Asalin hoton, Pushpa
Pushpa (a tsakiya) tare da wasu mata biyu masu lalurar gani da suka zo zana jarrabawa
“A yanzu zana jarrabawa ya zamo aikin yau da kullum. Bana gajiya da rubuta ta,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa hakan ya taimaka mata wajen koyon darusa da dama kama daga tarihi da kuma lissafi.
Baya ga rubuta wa masu lalurar gani jarrabawa, Pushpa, tana kuma taimakon ɗaliban da ke fama da lalurar laka da masu fama da nakasar da ke shafar tsokokin jikin mutum da kuma waɗanda suka samu raunuka da ba za su iya taɓuka komai ba.
Da farko, ta sha fama wajen gane maganar masu fama da lalurar laka.
“Dole ya kasance sai da na mayar da hankali sosai. Ina duba yadda laɓɓan bakinsu ke juyawa don gane abin da suke nufi.”
Duk da cewa ba ta fara da daɗi ba, daga baya Pushpa ta kasance cikin jerin ɗalibai da suka samu maki mai yawa, a wata jarrabawa da ta rubuta wa Karthik, wadda ke amfani da keke don yin tafiya.
“Na rubuta masa dukkan jarrabawarsa ta karshe a makaranta, gaba-ɗaya na rubuta darusa 47,” in ji Pushpa.
Asalin hoton, Pushpa
Pushpa tare da Karthik
“Lokacin da nake rubuta jarrabawa ta a makaranta, Pushpa ta zo don rubuta wa wani ɗalibi. Ina da wani wanda yake rubuta wa mutane jarrabawa, amma kwatsam sai ya tafi babu zato ba tsammani. Bayan kammala aikinta, Pushpa ta zo ta rubuta min ta wa jarrabawa,” in ji Karthik.
Ɗan shekara 25 ɗin ya ce ba zai misalta irin godiya da zai yi mata ba.
“Ba ma iya yin rubutu, kuma yawancin mu ba mu da ilimin kwamfuta saboda hannayen mu ba su da saurin rubutu.”
“Na yi sa’a da samun mutane irin Pushpa,” in ji Karthik.
Aiki tare na tsawon shekaru, ya ba su damar fahimtar juna – a yanzu Karthik ya kammala makaranta, yana kuma shirin zana jarrabawar ɗaukar aikin gwamnati.
“Na sha rubuta wa dalibai da yawa jarrabawa, kuma kowane yana labari na musamman,” in ji Pushpa.
Taimakon da ya sauya rayuwa
A mako na uku na watan Maris ta rubuta wa Bhoomika Valmiki, ƴar shekara 19 da ke jami’a jarrabawa.
Asalin hoton, Pushpa
Bhoomika Valmiki a ɓangaren hagu ta yaba wa Pushpa saboda jajircewarta da hazaka da kuma hakurinta da take da shi
A matsayinta na wadda ke da lalurar gani, Valmiki tana amfani da manhajar da ke sauya rubutu zuwa sauti wajen koyon darussanta, amma tsarin ilimin Indiya bai shirya yin amfani da irin manhajojin ba wajen rubuta jarrabawa.
“Zan iya ci gaba kawai a rayuwata idan Pushpa ta rubuta min,” in ji Valmiki.
“Pushpa tayi hak’uri ta jira har na gama rubuta amsoshina, ba ta taɓa ɗaga min hankali ba, inda take sake maimaita min amsoshina kafin ta rubuta.”in ji Valmiki.
Taimako yana da iyaka
Yawancin mutanen da ke neman taimakon Pushpa sun sha wahala sosai don shiga jami’a, duk da haka ta ce tausayinta ba zai lalata mata mutuncin ta ba.
Asalin hoton, Pushpa
Pushpa ta ce taimakonta yana da iyaka – ba za ta iya shiga tsakani ba idan ɗalibi ya yi kuskure
“Aikina shi ne rubuta abin da suka faɗa,”in ji Pushpa.
“Ba ni da zaɓi idan suka ce na rubuta amsar da ba daidai ba ko kuma faɗar kalmar da ba haka take. Ba zan iya wuce haka ba.”
“Wasu lokuta ɗaliban da ke magana da wasu harsuna na wahala wajen gane kalmomin ingilishi. Ina fassara musu kalmomin. Wannan shi ne taimakon da zan iya.”
Akwai mai sa ido guda ɗaya a kan kowane ɗalibi da kuma na’urar ɗaukar hoto. Ba a barin masu rubuta dalibai jarrabawa su zana duk wani darasi da suka koya a jami’a.
Mayar da alkhairi
Asalin hoton, Pushpa
Rubuta jarrabawa dabban-daban ya kuma taimakawa Pushpa wajen koyon abubuwa da yawa
Pushpa ta fito daga dangi matalauta kuma mahaifinta ya yi hatsari a wurin aikinsa. Mahaifiyarta ta yi aiki tuƙuru don ciyar da Pushpa da ɗan’uwanta.
“A wani lokaci ni da yayana mun dai na zuwa makaranta saboda ba za mu iya biyan kuɗi ba,” in ji ta.
Wani baƙo ne ya zo ya biya mana kuɗin. Pushpa ta ce aikinta na sa-kai yana biyan wannan da sauran ayyukan alheri.
Bayan sun gama makaranta, ita da ɗan uwanta suka soma aiki a wani kamfani mai aika sako. Pushpa ta yi digirinta na farko a fannin ilimi sannan ta kuma yi difloma a fannin kimiyyar kwamfuta.
Shekarun baya-bayan nan sun kasance masu wahala. A shekarar 2018 mahaifinta ya rasu. A 2020, ɗan uwanta ya mutu lokacin ɓarkewar annobar korona – har yanzu ba a san dalilin mutuwarsa ba.
Bayan shekara guda, Pushpa, wanda a lokacin ba ta da aikin yi, ta gamu da ƙarin labarai maras daɗi.
“A watan Mayun 2021, mahaifiyata ta rasu, bayan ‘yan watanni a watan Agusta, na rubuta jarrabawa 32. Wasu ranaku kuma, na kan rubuta jarrabawa biyu.”
Ta ce rubuta wa mutane jarrabawa ya taimaka mata wajen shawo kan baƙin cikin da take ciki.
Yaba wa kwazon Pushpa
Asalin hoton, Pushpa
Ƙasar Indiya ta yaba wa Pushpa kan aikin taimakon ɗalibai wajen rubuta jarrabawa da take yi
Aikinta na rashin gajiyawa bai tashi a banza ba, inda ta kai har ta lashe lambar yabo ta ƙasa saboda taimakon sauran mata.
“A ranar 8 ga watan Maris ɗin 2018, na sami lambar yabo daga shugaban ƙasar Indiya.”
Ta kuma gana da Firaminista Narendra Modi tare da sauran waɗanda suka samu lambar yabo.
A yanzu Pushpa tana aiki a cikin fasaha kuma tana ba karfafa gwiwa a cikin tarukan kamfanoni.
Asalin hoton, Pushpa
A yanzu Pushpa tana bayar da kalaman karfafa gwiwa a tarukan jama’a
Amma har yanzu tana rubuta jarrabawar wa waɗanda ba za su iya ba, kuma tana aiki da harsuna biyar (Tamil da Kannada da Ingilishi da Telugu da kuma Hindi) hakan na nufin ana bukatar taimakonta sosai.
“Ina ba da lokacina da kuzarina. Idan na rubuta jarrabawa ga wani, tana canza rayuwarsu,” in ji ta.