
Asalin hoton, SUPPLIED
Mrs Gifford ta shiga gidan ne tun tana da shekara biyu, har kuma ta hayayyafa
Wata mata a Somerset ta sayar da gida bayan ta kwashe shekara 102 tana zaune a cikinsa.
Matar ta haura karni guda tana zaune a wani gida, ta sa gidan a kasuwa.
A shekara 102 da Nancy `Joan` Gifford ta yi a gida mai dakin kwanciya uku a Somerset, a Somerset ne duniya ta shaida aka yi Yakin Duniya na Biyu, nan ne kuma aka kirkiri Talabijin da kuma sauka a duniyar wata.
Kudin da aka yi wa gidan £169,950 ya gaza £200 da iyayenta suka biya.
Duk da shekarun da gidan ya yi yawancin kayayyakin da suke cikinsa suna nan a yadda aka san su.
Dan Mrs Gifford, John mai shekaru 79, ya ce ya tashi ya girma a gidan – wanda aka gina shi a 1882 a unguwar – abu ne da za a iya cewa “tubarkalla”.
Asalin hoton, SUPPLIED
Bert da Nancy Gifford sun reni yaransu biyu a gidan bayan sun yi aure a 1939
Asalin hoton, SUPPLIED
“A wancan lokacin yawancin yara sa`o`inmu duk mun san juna, kuma gidan a bude yake ga kowa, kuma ba matsala ka bar kofarka a sakata,” kamar yadda ya bayyana.
“A lokacin dukkanmu talakawa ne, sannan kowa yana cikin farin ciki.”
Da Mrs Gifford ta tare tana `yar shekara biyu, kayayyakin da suke cikin dakin girki, da wajen ba-haya, da na sikola a bayyane suke, sai komi da ake shiga ciki a yi wanka da yake rataye a waje.
Tuni aka rufe wajen aka yi sabon dakin dahuwa, tare da karin wajen wanka na iyali, sai dai yawancin kayayyakin suna nan, sai wani dan fenti a farkon shekarun 2000.
Ta tashi ta girma a layin aka sa Mrs Gifford a Makarantar Katolika a Glastonbury, inda ta hadu da wanda ya zama mijinta, Bert, a tsakiyar shekarun 1930 a lokacin da take tafiya tare da kawayenta.
Asalin hoton, SUPPLIED
Bert da Nancy Gifford tare da ɗiyarsu Mary
Suka yi aure a lokacin da aka soma Yakin Duniya na Biyu a 1939, suka haifi `ya`ya biyu, Mary da John da har yanzun yana nan a unguwar tare da matarsa Sue.
Bayan yakin, Mr Gifford ya kwashe shekara 42 yana aiki a wata masana`anta ta Clarks a unguwar a matsayin mai daidaida dunduniyar takalma, matar kuma tana yi wa mai yin takalmi dinkin takalma.
Rashin lafiya ya tilasta wa Mrs Gifford ficewa daga gidan zuwa wani asibiti na St Benedict Glastonbury, dillalin gidaje Holland and Odam, da zai sayar da gidan ya yi bayanin.
Jack Bartram, manajan yankin unguwar, ya ce: “Dole wannan gida ya kasance yana da abubuwan tunawa masu dadi da yawan gaske ga Mrs Gifford da iyalanta, amma a yanzun, bayan fiye da karni, lokaci ne ya yi da wasu iyalan su ma za su shiga su kafa nasu abubuwan tunawar.”