Matar da ta tunatar da ‘yan Taliban muhimmancin ilimi da ayar Al-Kur’ani



Adela na zanga-zanga kan haramtawa mata ci gaba da karatun jami'a da gwamnatin Taliban ta yi a Afghanistan

Asalin hoton, Adela

Bayanan hoto,

Adela ta yi zanga-zangarta a gaban jami’ar Kabul, an kuma dakatar da ita a minti 15 da farawa

“Ban ce tsoro ko kadan ba, saboda na san abin da na yi kan hanya ya ke,” inji matashiyar ‘yar Afghanistan mai shekara 18 da babu alamar tsoro ko kadan tattare da ita, mai cike da burin ganin ta yi karatun jami’a, sai dai kash matakin gwamnatin Taliban ya sanya ta cikin matsananciyar damuwa saboda sun haramtawa mata zuwa jami’a.

Takaici da bakin cikin ganin mafarkinta na neman bin iska, da tasgaro da yi wa makomarta kafar ungulu, (mun sauya sunanta saboda dalilai na tsaro) ta dauki matakin yin zanga-zanga ita kadai a gaban jami’ar Kabul ta hanyar amfani da kalma daya daga Alkurani, wani lamari da ba safai ake gani ba.

Ranar 25 ga watan Disamba, Adela ta tsaya gaban babbar kofar shiga jami’ar dauke da allon da aka rubuta kalma daya ta harshen larabci- Iqra, ko kuma ”Karanta”. Musulmai sun yi imanin ita ce kalmar farko da Allah SWA ya fara saukar wa Annabi Muhammad SAW.

”Allah ya ba mu damar neman ilimi. Ya kamata mu ji tsoron Allah, ba ‘yan Taliban ba da ke son kwace ma na ‘yancinmu ba,” a hirar ta da BBC.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like