Matar Data Hallaka Mijinta Da Taɓarya A Jihar Neja


Ana zargin wata mata mai suna Balaraba da hallaka mijinta Malam Sani Doctor dake garin Kasanga a karamar hukumar Mashegu ta Jihar Neja ta hanyar bugun shi da tabarya wanda hakan yayi sanadiyyar rasa ransa.

Wani mazauni yankin mai suna Malam Nura Alhasan Jigawa ya shaida faruwar lamarin inda yace ” tsananin kishine yasa matar aikata haka saboda Sani Doctor nada mata uku ne biyu suna gida daya yayin da ita kuma take gidanta daban, sakamakon zuwa ganin sauran matan biyu da yaje yayi hakan yasa Laraba cewar ya wulakantar da ita wanda hakan yasa suka rika musayan yawu cikin bacin rai matar ta dauko tabarya ta buga mai nan take yafadi kasa tana ganin haka ta garzaya gidan sarkin garin ta shaida mashi abunda tayi, inda nan take aka kamata.

A kwanakin baya Malam Sani Doctor ya saki matar amma daga bisani suka shirya.

Yanzu haka dai matar na hannun jami’an tsaro inda suke cigaba da gudanar da bincike.

You may also like